1 John 1

Kalmar Rai

1Wannan da ya kasance tun farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa-wannan ne muke shela game da Kalmar rai. 2Ran nan ya bayyana, muka kuwa gan shi muka kuma shaida shi, muna kuwa yi muku shelar ran nan madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu. 3Muna yin muku shelar abin da muka gani muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi. 4Muna rubuta wannan domin farin cikinmu yǎ zama cikakke.

Tafiya cikin Haske

5Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa: Allah haske ne; kuma a cikinsa babu duhu ko kaɗan. 6In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. 7Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan
Ko kuwa kowane
zunubi.

8In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yǎ kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. 10In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.

Copyright information for HauSRK